1 Oktoba 2026 - 13:35
Source: Al-Mayadeen
Taswirorin "Google" Na Mummunar Barna A Gaza Bayan Shekaru 3 Na Yaƙin Kisan Kare Dangi + Hotuna

Sabbin hotuna daga taswirorin "Google" sun fallasa girman mummunar barna a Zirin Gaza da wahalar ɗan adam da 'yan gudun hijira ke fuskanta a cikin tantuna cikin shekaru 3 na yaƙin kisan kare dangi da isra’ila ke aiwatarwa.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Jaridar "The Guardian" ta Biritaniya ta ruwaito wasu sabbin taswirorin "Google" wanda ke fallasa girman barnar da isra’ila ta haifar a Zirin Gaza a cikin yaƙin cikin shekaru 3, da kuma haɗarin tabbarewar yanayin ɗan adam da mazauna ke ci gaba da fuskanta.

An ɗauki hotunan ne a watan Yuni na wannan shekara, kuma sun nuna ƙarin irin barnar da ta aukawa gidaje, kasuwanci, wuraren ibada da ababen more rayuwa tun bayan da dakatar da tsagaita wuta ta fara aiki a watan Oktoba 2025.

Taswirorin "Google" Na Mummunar Barna A Gaza Bayan Shekaru 3 Na Yaƙin Kisan Kare Dangi + Hotuna

Hotunan sun nuna manyan sansanonin tantuna da ke jere a kan babban ɓangare na bakin teku, galibi suna da nisan 'yan mitoci kaɗan daga teku.

Bisa ga hotunan, an nuno babbar tashar jiragen ruwa ta Gaza, wadda a baya take cike da zirga-zirga, ta zama mummunar kufai saboda lalacewa kuma babu kwale-kwalen kamun kifi ko daya, kewaye da wuraren zama na wucin gadi, kuma duk wani fili da ke buɗe a birnin Gaza cike yake da bukkoki da tantuna da gidaje marasa tsari.

Hotunan sun kuma nuna mummunar barna da ta shafi garuruwan arewa kamar Beit Lahia da Beit Hanoun, da kuma lalata wuraren ibada kamar Masallacin Al-Istiqlal a Khan Younis.

Taswirorin "Google" Na Mummunar Barna A Gaza Bayan Shekaru 3 Na Yaƙin Kisan Kare Dangi + Hotuna

Manyan unguwannin birnin Gaza, kamar Jabalia da Shujaiya, waɗanda aka kai musu hari akai-akai a hare-haren Isra'ila, yanzu sun zama marasa mazauna ba kowa.

Haka kuma, hotunan sun nuna ɗimbin wuraren tarkace a kudancin Gaza, inda da alama sojojin mamayar sun kawar da wani faɗin yanki a kan iyaka da Masar, kuma da alama an rushe birnin Rafah kusan gaba ɗaya yayi bai daya da kasa, kuma an rushr Tal al-Sultan ma da ban kasa.

A nata ɓangare, hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya ta taimaka wa 'yan gudun hijirar Falasɗinawa (UNRWA) ta bayyana cewa kusan kashi 82 cikin 100 na gine-gine sun lalace kuma an lalata kusan kashi biyu cikin uku na waɗannan gine-ginen, kuma fiye da 'yan gudun hijira miliyan 2.1 suna rayuwa cikin tanti da wuraren mafaka na wucin gadi a Zirin Gaza.

Taswirorin "Google" Na Mummunar Barna A Gaza Bayan Shekaru 3 Na Yaƙin Kisan Kare Dangi + Hotuna

Wani kiyasi na kwanan nan na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi hasashen cewa adadin gine-ginen da aka lalata a duk faɗin Gaza ya ƙaru da kashi 9 cikin 100 tun bayan sanarwar dakatar da wuta a watan Oktoba 2025.

A wannan fanni, wakilin musamman na shirin Majalisar Ɗinkin Duniya kan ci gaba a Falasɗinu Jaco Cilliers ya gaya wa jaridar "The Guardian" cewa jimillar adadin tarkacen baraguzai an kiyasta da kaiwa tan miliyan 61.

Taswirorin "Google" Na Mummunar Barna A Gaza Bayan Shekaru 3 Na Yaƙin Kisan Kare Dangi + Hotuna

Ya bayyana cewa wannan ya kai kusan sau 20 na adadin tarkacen da duk yaƙe-yaƙen duniya suka haifar cikin shekaru 18 da suka gabata, yana mai nanata cewa kasancewar gawarwakin ɗan adam da aka binne a ƙarƙashin tarkace na daga cikin matsalolin ɗan adam da suka fi bukatar gaggawa.

…………..

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha